NDC: Lauya ya zargi wasu jiga-jigan jam’iyya Kano da tsoratarwa, ya kare Sha’aban, Nasir da sauran ’yan takarar

Imgonline com ua twotoone ChFL7xwDAblK5dS 750x430

Wani ofishin lauyoyi da ke wakiltar ’yan takara biyar na jam’iyyar NDC a Jihar Kano, ya zargi wasu jiga-jigan jam’iyyar da kokarin kawo cikas ga takarar wadanda yake wakilta ta hanyar tsoratarwa ta siyasa, shirya zanga-zanga da kuma shigar da korafi kan wani jami’in Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, wadda babban lauyan kfishin, Bola Aidi SAN, ya sanya wa hannu, ya bukaci INEC, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su mutunta hukuncin kotu da ya tabbatar da takarar wasu biyu daga cikin wadanda yake wakilta, tare da barin shari’o’in da ke gaban kotu kan sauran ’yan takarar su gudana ba tare da tsoma baki ba.

Lauyoyin suna wakiltar Abdulmajid Isah Umar, wanda ke neman kujerar Majalisar WakilaI a Gwale, Sha’aban Ibrahim Sharada na Kano Municipal, Barr. Ishmael Idris Sani na Kumbotso, Ibrahim Bashiru Bango na Sumaila/Takai da Nasir Alli Ahmed na Nasarawa.

Lauyan ya ce ’yan takarar biyar sun samu tikitinsu ne ta hanyar bin hanyoyin da jam’iyyar ta tanada na tsayawa takara, wadanda suka hada da bayyana sha’awar tsayawa takara, tantancewa, amincewa, cancanta da kuma zaben fidda gwani.

Sanarwar ta kara da cewa Kwamitin Daukaka Kara na 01, wanda aka kafa bisa tanadin kundin tsarin mulkin NDC da ka’idojin zaben fidda gwani na jam’iyyar, shi ma ya sake tabbatar da takarar ’yan takarar.

Sanarwar ta biyo bayan wani korafi mai kwanan watan 16 ga Oktoba, wanda ake zargin ofishin lauyoyi na Tahir Chambers ya rubuta a madadin reshen NDC na Jihar Kano, kan wata jami’ar INEC mai suna Mrs Hauwa Buhari, bisa zargin kura-kurai a rahotannin da suka shafi zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Lauyoyin sun nuna shakku kan lokacin da aka shigar da korafin, wanda ya ce ya zo ne kwanaki biyu bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin tabbatar da takarar wasu biyu daga cikin wadanda yake wakilta.

A cewar lauyoyin, korafin da zanga-zangar baya-bayan nan ba sa wakiltar matsayar shugabancin jam’iyyar na jiha, inda suka kara da cewa shugaban jam’iyyar da wasu shugabanni ba su da masaniya kan zarge-zargen da aka yi wa jami’ar INEC.

“Wadanda muke wakilta sun tabbatar da cewa sun samu takararsu ne ta bin hanyoyin da NDC ta tanada yadda ya kamata.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here