Farashin mai ya haura Dala 100 yayin da Iran ta yi barazanar rufe mashigar Hormuz

2026 03 12t083158z 762418261 rc2w2kajxoai rtrmadp 3 iran crisis iraq tankers 750x430

Farashin danyen mai ya ci gaba da kasancewa sama da Dala 100 a ranar Juma’a, yayin da yawancin kasuwannin hannayen jari suka ragu bayan jagoran Iran ya yi kira da a rufe muhimmin mashigar ruwan Strait of Hormuz tare da bude sabbin fagage na yaki da Amurka da Isra’ila.

Yayin da rikicin ya shiga mako na uku ba tare da alamun kawo karshensa ba, masu zuba jari suna kara fargabar cewa rikicin zai iya tsawaita, wanda hakan zai kara hauhawar farashi tare da jefa tattalin arzikin duniya cikin matsin lamba.

Tehran ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi a yankin tekun Gulf a wannan makon, inda aka kai hari kan jiragen ruwa kusa da Iraki, aka kai hari kan tankunan mai a Bahrain, sannan aka harba jiragen sama marasa matuki zuwa wuraren hako mai a Saudi Arabia.

Haka kuma Iran ta yi gargadin cewa za ta “kunna wuta a dukkan mai da iskar gas na yankin” idan aka kai hari kan cibiyoyin makamashinta da tashoshin jiragen ruwa.

A jawabinsa na farko ga jama’a tun bayan da ya gaji mahaifinsa kwanaki hudu da suka gabata, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya ce dole ne mashigar ruwan Strait of Hormuz ta kasance a rufe.

Ya kuma kara da cewa an gudanar da nazari kan bude wasu sabbin wuraren yaki inda abokan gaba ba su da kwarewa sosai kuma za su kasance masu rauni, kuma za a fara amfani da su idan yakin ya ci gaba.

Farashin danyen mai ya tashi da fiye da kashi tara cikin dari a ranar Alhamis, inda danyen mai na Brent ya kare sama da Dala 100 a karon farko tun shekarar 2022 lokacin da Rasha ta kaddamar da mamayar Ukraine.

Farashin Brent ya karu da kusan kashi 40 cikin dari tun bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya a ranar 28 ga Fabrairu.

Har ila yau farashin ya ci gaba da kasancewa a wannan matakin a kasuwannin ranar Juma’a da safe, inda masana suka ce sakin gangar danyen mai miliyan 400 daga rumbunan ajiyar Hukumar Makamashi ta Duniya bai yi tasiri sosai ba.

Hukumar Makamashi ta Duniya ta bayyana a ranar Alhamis cewa yakin yana haifar da babbar tangarda wajen samar da mai a tarihin kasuwar danyen mai ta duniya.

A gefe guda kuma, shugaban Amurka Donald Trump yana fuskantar matsin lambar siyasa yayin da tasirin rikicin ke kara tabarbarewar tattalin arzikin duniya, duk da cewa kasuwanni sun yi watsi da ikirarin da ya yi cewa yakin ba zai dauki lokaci mai tsawo ba.

Shugaban Amurka ya bayyana a wani sako da ya wallafa a kafafen sada zumunta cewa Amurka ita ce kasa mafi girma wajen samar da mai a duniya, don haka idan farashin mai ya tashi suna samun riba mai yawa.

Sai dai ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci a gare shi a matsayinsa na shugaban kasa shi ne dakatar da Iran daga mallakar makaman nukiliya da kuma hana ta lalata Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.

Chris Weston na kamfanin Pepperstone ya bayyana cewa kasuwanni suna kara sanya hasashen cewa rikicin zai dauki lokaci mai tsawo, musamman idan har aka rufe mashigar Strait of Hormuz.

Ya kuma kara da cewa Donald Trump na iya ci gaba da duba yiwuwar taimakawa jiragen ruwa su rika wucewa ta mashigar, wanda idan hakan ta faru kasuwa na iya samun sauki.

Sai dai a halin yanzu manyan abubuwan da ke jan hankali su ne karin farashin makamashi da kuma girgizar kasuwanni.

Yayin da damuwa ke karuwa kan tasirin rikicin, ‘yan kasuwar hannayen jari suna janyewa daga kasuwa, musamman a kasashen Asiya da suka fi dogaro da shigo da makamashi.

Kasuwannin hannayen jari a Tokyo, Hong Kong, Shanghai, Singapore, Seoul, Mumbai, Bangkok, Wellington, Manila da Jakarta duk sun ragu.

Dalolin Amurka ya ci gaba da samun karfi a kan manyan kudaden duniya saboda matsayinsa na kudin da ake neman mafaka da shi a lokutan rikici, da kuma fargabar hauhawar farashi tare da hasashen cewa kudin ruwa zai ci gaba da kasancewa a sama na wani lokaci.

Matt Weller, shugaban binciken kasuwa a kamfanin City Index, ya yi gargadin cewa kasuwanni na iya fuskantar karin matsin lamba bayan shekaru da aka shafe ana samun karuwar kasuwannin hannayen jari da kuma saukin farashin makamashi da kuma karancin kudin ruwa.

Ya ce wadannan abubuwa sun sauya, kuma matukar mashigar Strait of Hormuz ta ci gaba da kasancewa a rufe, ana sa ran kasuwannin hannayen jari za su kasance cikin matsin lamba, farashin mai zai ci gaba da tashi, sannan kudin ruwa zai karu tare.

Ya kara da cewa sai idan an samu ci gaba mai ma’ana wajen tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya, masu kasuwa su shirya cewa makonni da watanni masu zuwa za su bambanta da shekaru biyun da suka gabata, wanda hakan zai kara rage sha’awar zuba jari cikin hadari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here