Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 18 da 21 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu don baiwa Kiristoci damar gudanar da bukukuwan Easter.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar harkokin cikin gida, Misis Magdalene Ajani, ta fitar ranar Talata a Abuja.
Ajani ta ce ranakun hutun da jama’a za su yi na bukukuwan sun hada da ranar Juma’a da kuma ranar Litinin.
Ta ce, ministan harkokin cikin Gida, Dskta Olubunmi Tunji-Ojo, ya mika sakon taya murna ga mabiya addinin Kirista a fadin kasar nan kan bukukuwan, har ma ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin hutun wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da kwanciyar hankali.
Ministan ya kara tabbatar wa ‘yan kasar nan irin jajircewar shugaban kasa Bola Tinubu kan bunkasa ci gaban su da ci gaban kasa.NAN)