Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta tabbatar da ƙudirinta na samar da kimanin bindiga 7,000 domin bai wa wasu ƴan sintiri da za ta zaƙulo daga cikin al’umma don aiwatar da wani tsari da ta kira “Carrot and Stick Approach” don fatattakar ƴan bindigar da suka ƙi miƙa wuya.
Mai bai wa gwamnan Zamfara shawara kan harkokin yaɗa labarai, Zailani Baffa ne ya bayyana hakan ga BBC inda ya ce matakin da ake kai yanzu a wannan tsarin shi ne za’a ci gaba da yaƙar waɗanda suka bijriewa sulhu, kamar yadda gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin a zafafa yaƙarsu.
A cewarsa, matakin zai shafi kowane yanki da ƙauyukan da ke da matasa, da sarakunansu suka amince mutanen kirki ne, (Shugabannin Ƙananan hukumomi) za su ba da amincewarsu.
“Gwamnati za ta taimaka musu su samu makamai daga hannun ƴan sanda irin makaman da gwamnatin tarayya ta yadda waɗanda ba irinsu ƴan sanda ko sojoji ke amfani da su ba.”
Ya ce ko a ƴan watannin baya-bayan gwamnatinsa ta sanar da burinta na bai wa ƴan jihar da kuma waɗanda ke zaune a jihar damar neman lasisin riƙe bindiga domin kare kansu daga hare-haren masu tayar da zaune tsaye.













































