Bayan cika shekaru 35, Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da barikin NDLEA a Yola

WhatsApp Image 2025 02 18 at 15.54.59 750x430

Shekaru 35 bayan kafa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, a yau Talata ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da bariki na farko da za ta samar da ofishi da matsuguni ga jami’ai maza da mata na hukumar yaki da muggan kwayoyi.

SolaceBase ta ruwaito cewa da yake magana a wajen bikin kaddamar da barikin NDLEA na farko a Yolan jihar Adamawa, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya ce ginin wanda ya hada da ofisoshin gudanarwa na zamani, da wuraren zama, zai taimaka wajen samar da kyakkyawan yanayi gudanar da ayyukan hukumar da kuma kyautata rayuwar iyalan ma’aikan cikin mutunci da tsaro.

A cewar wata sanarwa da daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hedikwatar NDLEA ta Abuja ya fitar, babban lauyan gwamnatin tarayya ya ce, “Ba za a iya wuce gona da iri kan rawar da NDLEA ke takawa a cikin al’ummarmu ba domin yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi yaki ne ga makomar kasarmu da matasanmu daga mummunar illar shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma kawar da al’ummarmu daga tashe-tashen hankula da ma fataucin miyagun kwayoyi”.

Ya bukaci jami’an NDLEA da za su zauna a barikin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu wajen yi wa kasa hidima.

Yayin da yake yabawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a karkashinsa aka amince da aiwatar da aikin, Ministan ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa taimakon tabbatar da wannan aikin da kuma gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa bisa kyakkyawan hadin kai da goyon bayansa wajen ganin an gudanar da aikin cikin yanayi mai kyau da kwanciyar hankali, kamar dai yadda ya yaba da goyon bayan da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na NDLEA Ribadu ya samu.

A nasa jawabin, Shugaban jukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya jaddada muhimmancin aikin bariki ga tsaron lafiyar ma’aikatan Hukumar shekaru 35 da kafa ta. “Wannan shekarar ce ta cika shekaru 35 da kafa hukumar NDLEA. Tsawon shekaru, rashin wurin zama na musamman ga jami’an mu ya haifar da kalubale, gami da fuskantar haɗari ga su da iyalansu. Abin takaici, an bi diddigin ma’aikatanmu da dama zuwa gidajensu tare da kashe su. Irin wadannan al’amura sun jaddada muhimmancin samar da gidaje masu tsaro ga ma’aikatanmu.”

Karin karatu: NDLEA ta tarwatsa dandalin shaye-shaye tare da kama mutane 18 a Kano

Ya bayyana matukar godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da goyon baya da kuma imani da hukumar ta NDLEA.

A sakon da ya gabatar a wajen taron, Gwamna Ahmadu Fintiri ya yabawa shugaba Tinubu, da Marwa da sauran masu ruwa da tsaki bisa hangen nesa da jajircewarsu kan aikin samar da bariki.

“Wannan bariki wata shaida ce ta sadaukarwar da suka yi na ceto al’ummarmu da al’ummarta, musamman matasanmu, wadanda su ne manyan kadarorinmu da jagororinmu na gobe daga tarin miyagun kwayoyi”.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a jawabinsa wanda AIG Rex Dundun ya gabatar ya ce “wannan babban ci gaba yana kara jaddada kudirin gwamnatin tarayya na samar da yanayi mai kyau ga hukumomin tsaron kasar nan.

Hukumar NDLEA tana taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye lafiyar al’ummarmu, aminci da walwala ta hanyar yakar barazanar fataucin muggan kwayoyi da kuma cin zarafi don haka dole ne a yaba wa shugaban jukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd) da tawagarsa bisa namijin kokarin da suka yi wajen jagorantar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya.”

Shima da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin majalisar dattawa akan sha da fataucin miyagun kwayoyi, Sanata Ibrahim Dankwambo ya bayyana cewa “aikin jami’ai da jami’an hukumar ta NDLEA na bukatar hadin kan al’ummar ganowa da aiwatar da doka, wanda ke bukatar samar da isasshen kwarin gwiwa ga ma’aikata.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da Miyagun Kwayoyi Abass Adigun wanda mataimakin shugaban kwamitin Idris Dankawu ya wakilta, ya ce tabbatar da tsaro da jin dadin ma’aikatan NDLEA ba abin wasa bane ya zama wajibi, ya kara da cewa majalisar wakilai za ta ci gaba da tsayawa wajen bayar da shawarwarin samar da ingantattun kudade, inganta yanayin aiki, da kuma kara karfin gudanar da ayyukan hukumar.

Sauran manyan baki da suka halarci bikin sun hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Sanata Francis Fadahunsi, ‘yan majalisar dokoki ta kasa daga jihar Adamawa, da sarakunan gargajiya masu daraja ta daya daga sassan jihar da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here