Wani mummunan hatsari ya auku a daren Juma’a a jihar Ogun, lokacin da wata babbar motar siminti mallakar kamfanin Dangote ta buge wata Adaidaita Sahu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar da ke cikinta nan take.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 8:30 na dare a yankin Alapoka, kan titin Papalanto–Ilaro da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu.
Mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da cewa hatsarin ya rutsa da wata Adaidaita Sahu marar lamba da kuma babbar motar Dangote mai lamba GRZ 767 XA.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa dalilin hatsarin shi ne gazawar birki daga babbar motar.
Shaidu sun bayyana cewa direban motar bai ma sanin cewa ya yi hatsari ba sai bayan da motar ta murƙushe Adaidaita Sahun da fasinjojin cikinta baki ɗaya.
Jami’an TRACE karkashin jagorancin mukaddashin shugaban hukumar, Adedayo Omonayajo, da kwamandan sashen Ilaro, Salako Idowu, sun isa wajen domin gudanar da aikin ceto.
Sai dai aikin ya samu tsaiko na ɗan lokaci sakamakon fushin mazauna yankin, kafin dakarun Amotekun su shawo kan lamarin.
A ƙarshe, jami’an hukumar kiyaye hadura ta tarayya (FRSC) ne suka ɗauki gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa dakin ajiye gawa.












































