Hukumar Gudanarwa ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe (YSUTH) ta samu gagarumar nasara a fannin lafiya biyo bayan nasarar gudanar da tiyatar sauya kugu gaba daya (total hip replacement surgery) a kan wani matashi.
An gudanar da tiyatar ne a ranar Asabar a kan wani mara lafiya da ke dauke da cutar amosanin jini (sickle cell disease), wanda ya fuskanci matsalar mutuwar kashin kugu sakamakon rashin isar isashshen jini zuwa samfurin kashin cinyarsa.
Read also: Najeriya ta tsananta tsaro kan iyakokinta saboda cutar Ebola
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, kwararren likitan nan, Dr Lawan Yari, ne ya jagoranci wannan kebantacciyar tiyata, tare da taimakon Dr Musa Abdulmalik, Dr Bashok Palagvi, Mista Manasseh Jonah da kuma Mista Karumi Ibrahim.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Muhammad Gana, wanda ya yi wa manema labarai bayani kan wannan ci gaba a ranar Lahadi, ya bayyana cewa a fannin lafiya ana kiran wannan rashin lafiya da avascular necrosis.
Read also: Kamaru ta zama kasar farko da ta kaddamar da gangamin rigakafin cizon sauro
Ya bayyana tiyatar a matsayin wata gagarumar nasara mai cike da tarihi, inda ya ce tiyatar sauya kugu baki daya wani aiki ne na fida inda ake cire gwiwar kugu da ta lalace a mayar da ta roba.
Ya bayyana cewa, a baya ba a samun irin wannan aiki a jihar ba, inda ya jinjina wa asibitin saboda gudanar da wannan tiyata mai wuyar gaske.
Ya bayyana cewa, a watan Mayun wannan shekara, Asibitin Kwararru na Jihar Yobe shi ma ya samu gagarumar nasara lokacin da ya yi nasarar gudanar da wata babbar tiyatar fuska da wuya.
Read also: Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 732 cikin kasafin kudin 2024 na karfafa wasu ayyuka
A fannin likitanci, ana kiran wannan tiyata da “maxillofacial”, kuma an yi ta ne a kan wata uwa mai shekaru 40 da aka gano tana dauke da wata kansa mai wuyar gaske wanda ba ta daji ba (non-cancerous tumour) da ta girma a kashin mukamukinta na kasa.
Ya danganta wadannan nasarori guda biyu ga irin goyon bayan da Gwamna Mai Mala Buni yake ba asibitin da kuma samar da ingantattun kayan aiki na zamani a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar. (NAN)















































