Tsohon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano, Sani Kofar Mata ya rasu

IMG 20260920 WA0279 750x430

Tsohon Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, ya rasu.

Majiyoyi masu inganci sun shaida wa SolaceBase cewa Kofar Mata ya rasu ne a yammacin Lahadi a Kano sakamakon rashin lafiya.

Marigayi dan siyasan abokin Malam Ibrahim Shekarau ne a jam’iyyar ANPP kuma ya shahara sosai a lokacin zaben gwamna na 2007.

Daga baya marigayin ya bar ANPP a 2011 tare da sauran manyan mambobin jam’iyyar kafin daga bisani ya koma jam’iyyar ACN.

SolaceBase ta tabbatar cewa za a gudanar da sallar jana’izarsa a gobe Litinin da misalin karfe 9.00 na safe a gidansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here