An gudanar da sallar jana’izar Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar NRC, Alhaji Bashir Tofa a gidansa dake unguwar Gandun Albasa a cikin birnin Kano.
Sheik Shehu Tijjani na ‘yan mota shine ya jagoranci sallar jana’izar da misalin karfe 9:20 na safiyar yau litinin.
Wanda suka halarci sallar jana’izar sun hada da mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da tsohon ministan noma Sabo Nanono da sauran manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan.
Solacebase ta ruwaito cewa marigayi Alhaji Bashir Tofa ya rasu ne da asubahin yau litinin bayan wata gajeriyar jinya.
Marigayin ya rasu yana da shekara 74 bayan da a ka haife shi a ranar 4 ga watan Yuni, a shekarar 1947.
Ƙarin bayani na nan tafe….
A makon da ya gabata ne dai a ka fara raɗe-raɗin cewa Tofa ya rasu, in da dangin sa su ka tabbatar da cewa bai rasu ba, amma bashi da lafiya.













































