An kama malaman makaranta a Kenya suna koya wa dalibansu yadda ake jima’i

FB IMG 16753288911844476
FB IMG 16753288911844476

‘Yan sanda a Kenya sun kama malaman makarantar firamare shida a yammacin kasar bayan da aka gansu cikin wani bidiyon da ake yadawa kamar wutar daji da ke nuna dalibansu na kwaikwayon yadda ake jima’i.

Kafofin yada labarai a yankin na cewa an kama malaman makarantar da ke Nyamanche a karamar hukumar Kisii, bayan da jami’an ma’aikatar ilimi ta kasar suka kai karar malaman bayan sun kalli bidiyon.

Ana iya ganin wasu manyan mutane cikin bidiyon na magana kuma suna dariya da karfi yayin da wani ke daukar hoton dalibai maza hudu da ke sanye da kayan makaranta.

Wani rahoton ‘yan sanda ya lura cewa bidiyon “ya budewa yaran idanunsu ga wata mummunar halayya”, kuma ba shakka daga makarantar bidiyon ya fito.

‘Yan sandan sun ce ana binciken yadda al’amarin ya auku.

Bidiyon ya haifar da kace-nace a shafukan sada zumunta, inda wasu ke neman a dauki matakan ladabtarwa kan wadanda aka samu da laifi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here