Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun ce akalla mutum 25 ne aka kashe a wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
An kai harin ne a garin Dikwa wanda ke kusa da garuruwan da ‘yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram ke da karfi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tun 2009, hare-haren kungiyoyi masu tsassaurar ra’ayi ya kashe mutane sama da 350, 000 da ɗaiɗaita miliyoyi.













































