Zakarun gasar cin kofin duniya, Argentina sun isa filin jirgin sama na Buenos Aires inda dubban jama’a suka fito domin yi musu maraba.

Gwamnatin kasar ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwa.
Magoya bayan kasar sun yi jerin gwano a kan titunan kasar domin yi musu maraba.

Nan gaba a ranar Talata ne za a gudanar da babban biki.
Lionel Messi ne ya soma fitowa daga cikin jirgi kafin sauran ‘yan kwallon kasar.














































