Dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura wato A.A Zaura ya sha alwashin ci gaba da kokarin ganin ya cimma burinsa na siyasa.
Da yake jawabi ga manema labarai ranar Laraba a hedikwatar yakin neman zaben sa dake kan titin Zaria, Zaura ya ce an kammala gudanar da rangadin yakin neman zabe a fadin unguwanni 172 da kananan hukumomi 15 da suka hada mazabar Sanata.
Jigon na APC ya ce yana da kwarin guiwar samun nasara a zabukan da za a gudanar ta yadda ya gudanar da ayyuka da dama wadanda suka yi tasiri ga rayuwar al’umma.
“Ni ba sabon yankan rake ba ne a siyasa, ban taba zuwa ba amma na gudanar da dubban ayyuka wadanda nake takara da su ba su yi kwata kwata ba. Kwankwaso da Shekarau sun yi nasu zamanin, sun yi iya kokarinsu amma ni nazo da wani sabon salo na musamman.
“Jama’ar Kano ta tsakiya sun yi sha’awar ganina a cikin Majalisa, Idan aka zabe ni, sauke bukatunsu shine babban alhakinmu.
“Ba abin da zai hana ni, ko ya tsoratar da ni in kasance tare da jama’ata. Kuma ba wata barazana ko matsi da za ta raba ni da talakawa, jama’a da talakawa. Su nawa ne, Kuma ni na sune,” in ji Zaura.
Jigon na APC ya yabawa kokarin gwamnatin jihar a fannonin kiwon lafiya, ilimi, tituna, noma, ababen more rayuwa, ci gaban bil Adama da dai sauransu.













































