Gwamnatin tarayya ta fara gangamin wayar da kai na kwanaki 16 game da cin zarafin jinsi

images 2 10
images 2 10

Ministar harkokin mata Uwargida Pauline Tallen, ta kaddamar da gangamin shirin zagayen wayar dakai na ‘kwanaki 16 a fafutukar yaki da cin zarafin mata a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da Tallen ta fitar, ta ce tashe-tashen hankula da ambaliyar ruwa na baya-bayan nan sun kara yawan cin zarafin mata a kasar.

Gangamin na ‘kwanaki 16, wani yunkuri ne da akeyi shekara-shekara da nufin magance matsalolin cin zarafin mata da ‘yan mata.

Ana fara gangamin ne kowacce shekara a ranar 25 ga watan Nuwamba kuma za a shafe kwanaki 16 har zuwa ranar 10 ga Disamba, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke bikin ranar ‘yancin dan Adam.

“Yau ne farkon kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata. Najeriya ta bi sahun kasashen duniya Wanda akayi masa taken: Yunkurin kawo karshen cin zarafin mata da ‘yan mata,” in ji Tallen.

Ministan ta fara taron ne dayin shiru na minti daya ga mutanen da suka mutu sakamakon tashin hankali.

Daganan ta yabawa dukkan abokan huldar da suka ba su goyon baya, inda ta kara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da karfafa aiwatar da tsare-tsare don samar da kariya ga masu rauni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here