Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, ya bayayana cewa dukkan shirye-shirye sun kammala domin fara yakin Neman zaben Shugaban Kasa a APC.
Lalong, Wanda shi ne Darakta Janar na yakin Neman zaben Shugaban Kasa na APC a Shekarar 2023 ya bayyana hakan ne lokacin da yake duba aikin Hedikwatar yakin Neman zaben Jam’iyyar a Abuja.
Gwamnan ya kuma gana da wasu mambobin kwamitin yakin neman zaben, a kokarin tabbatar da cewa komai ya tafi yadda ya kamata.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Dakta Makut Maham, ya fitar ranar Asabar a Jos, ya bayyana cewa sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mista James Faleke, ne ya tarbi gwamna Lalong a hedikwatar.

“Darakta Janar din ya kuma yi ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu a hedikwatar.
“Bayan nan Kuma sun sake yin wata ganawa da kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila da wasu ‘yan majalisar dokoki daga majalisar dokokin jihar,” in ji shi.











































