Gwamnatin Somaliya ta nada Kwamandan Al-shabab a matsayin Minista

Former al Shabaab group co founder and spokesperson Mukhtar Robow 1
Former al Shabaab group co founder and spokesperson Mukhtar Robow 1

Firaministan Somaliya Hamza Abdi Barre, ya nada wani kwamandan kungiyar al-Shabaab a matsayin ministan harkokin addini, matakin da ko dai zai taimaka wajen karfafa yaki da masu tada kayar baya ko kuma tada rikicin kabilanci.

Mukhtar Robow, yana da dalar Amurka miliyan 5 bayan da ya kafa kungiyar al-Shabab mai alaka da al Qaeda sannan ya zama kakakin kungiyar.

‘Yan ta’addar Al Shabaab sun kashe dubun-dubatar mutane a hare-haren bama-bamai a yakin da suke yi na hambarar da gwamnatin tsakiyar Somaliya da ke samun goyon bayan kasashen yammacin Turai.

A shekarar 2013 ne Robow ya balle daga kungiyar kuma ya yi tir da al-Shabab a bainar jama’a lokacin da ya zo bangaren gwamnati a shekarar 2017.

Amma dangantaka ta yi tsami bayan da ya shiga siyasa.

Gwamnatin da ta gabata ta Somaliya ta kama Robow a watan Disambar Shekarar 2018 a lokacin da yake yakin neman zaben shugaban kasa a yankin kudu maso yammacin kasar.

Jami’an tsaro sun harbe akalla mutane 11 a zanga-zangar da ta biyo baya.

Nadin nasa zai iya taimakawa wajen karfafa dakarun gwamnati a yankinsa na Bakool, inda masu tada kayar baya ke rike da yankuna masu yawa amma kuma Robow ya ba da umarnin tallafawa.

Sabon shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud, wanda ‘yan majalisa suka zaba a watan Mayu, ya yi alkawarin yakar masu tada kayar baya, a fadin Kasar.

A makon da ya gabata an kashe mayakan al Shabaab da dama da jami’an tsaron Habasha a fadan da aka yi a kan iyakar kasashen biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here