Ƴan ta’adda sun sace wani DPO a Kaduna

Nigeria Kidnappings Bandits deputy 1
Nigeria Kidnappings Bandits deputy 1

Wasu ƴan ta’adda sun yi awon gaba da wani sabon jami’in ɗan sanda mai muƙamin DPO Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Kamar yadda yadda Daily Trust ta ruwaito, an sace DPO ɗin ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin ƙarfe 9:00 na safe yau Litinin.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa DPO ɗin na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kai rahoto a bakin aikinsa lokacin da aka sace shi.

Babu tabbas ko jami’in yana tafiya shi kaɗai a cikin mota lokacin da aka ɗauke shi.

Har yanzu dai ƴan sanda ba su mayar da martani ko kuma fitar da wata sanarwa a hukumance kan sace shi ba.

Da aka tuntuɓi Mohammed Jalinge, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar ya ce, “Muna bincike kuma za mu magantu.”

Lamarin ya faru ne kwanaki huɗu da sace wani DPO a jihar Nasarawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here