Hukumar NUC ta sahalewa Jami’ar Wudil fara sabin darusa 21

KUST WUDIL
KUST WUDIL

Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa NUC ta bada cikakkiyar damar gudanar da wasu sabbin darusa 21 a tsangayoyin karatu 5 na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake garin Wudil.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa hukumar ta NUC ta sahalewa Jami’ar gudanar da darusan ne da nufin fadada koyo da koyarwa, bayan bincike da kuma la’akhari da irin kwararrun ma’aikata da ingantattun kayan aikin zamani da ake da su don yaye kwararrun Dalibai.

A cikin takardar amincewa mai kwanan wata 14 ga watan Afrilun 2022 mai dauke da sa hannun babban sakataren hukumar NUC, Farfesa Abubakar Abdulrasheed, ta hannun Darakta mai kula da aikin tantancewa, Dakta Maryam Sali, hukumar tace sahalewar sabbin darusan na nan har zuwa shekaru biyar masu zuwa.

Wasu daga cikin sabbin darusan, sun hada da: BSc. Ed. Agriculture da BSc. Ed. Biology da BSc. Ed. Chemistry da BSc. Ed. Physics sai BSc. Ed. Geography da Health Education BSc. Human Kinetics da kuma BSc. Library and Information Science.

Sauran sun hada da Civil Engineering da Electrical Engineering da Food Science and Technology sai Urban and Regional Planning da Biology da Chemistry da Geology sai Mathematics da Microbiology da Physics da Statistics da kuma Computer Science.

A baya-bayan nan dai jami’ar ta Wudil ta samu sahalewar hukumar NUC domin fara sabbin darusan digiri na 2 (Master’s Degree) guda 14 a makarantar.

Sahalewar ta biyo bayan bukatar da Jami’ar ta nema na bata cikakkiyar damar koyar da darusan.

Da yake magantuwa kan ci gaban shugaban jami’ar Farfesa Shehu Alhaji Musa ya bayyana cewa sahalewar da hukumar NUC ta yi karkashin jagorancinsa wata babbar nasara ce da za ta ci gaba da kasancewa cikin kankanin lokaci.

Sanarwar da mai magana da yawun Jami’ar ta Wudil, Sa’idu Na Yahaya ya fitar a ranar Asabar, yace shugaban Jami’ar ya bayyana gamsuwarsa da nasarorin da aka samu a shekarun da suka gabata, bisa goyon baya da jajircewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here