An yi garkuawa da ‘Ya da Uwa bayan kammala rabon kayan Tallafi ga marasa karfi a Kaduna

20220424 113548
20220424 113548

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuni da cewa an yi garkuawa da tsohuwar shugabar sashin, Electrical and Electronics Engineering na makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna, Dakta Ramatu Sangei, wadda aka fi sani Misis Abarshi.

Misis Abarshi, wadda tsohuwar mai dakin marigayi Air Commodore A. Abarshi ce kuma yanzu haka ita ce shugabar Kungiyar rajin tallafawa mata da matasa da kuma masu karamin karfi wato Barkindo Rahama Initiative, an yi garkuawar ne da ita tare da ‘Yar ta Ameera.

Wasu majiyoyi daga iyalanta sun bayyana cewa an yi garkuawar ne dasu bayan sun gama rabon kayayyakin tallafi a garin Mariri na karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna a lokacin da suke komawa suna kusa da Kasuwan Magani dake Kajuru Local ta jihar Kaduna.

“Suna kan hanyar su ne ta dawowa Kaduna lamarin ya faru, saboda haka muna bukatar addu’ar kowa da kowa albarkacin wannan wata na Ramadan”. Inji Habibu Sangei.

Kawo lokacin da muke rubuta labarin Rundunar ‘Yan sanda bata ce komai kan lamarin ba.

Jaridar Dateline Nigeria ta rawaito cewa Misis Abarshi ta gudanar da ayyukan da suka shafi bada horon sana’o’in dogaro da kai a madadin makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna, wadda yanzu haka babbar Malama ce a ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here