Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa wata gobara ta lakume gine-gine shagonan Plaza shida a sashin sayar da robobi na Babban Layi da ke Kasuwar Kofar Wambai a jihar.
Darakta Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar Asabar a Kano.
Anas ya ce lamarin ya faru ne a daren Juma’ar da ta gabata, inda ya kara da cewa hukumar ta karbi kiran gaggawa game da gobarar da misalin karfe 9:43 na dare.
Ya bayyana cewa daya daga cikin manyan jami’an hukumar, Usman Idris-Fagge, ne ya yi kiran gaggawar ta hanyar sashen kula da ayyukan gaggawa na hukumar.
Ya ci gaba da cewa nan da nan hukumar ta tura jami’an kashe gobara daga rassa daban-daban zuwa kasuwar domin shawo kan gobarar tare da hana ta bazuwar ta zuwa sauran shagunan.
Anas ya ce lokacin da jami’an kashe gobarar suka isa wurin, sun tarar cewa kusan gine-gine shida ne gobarar ta shafa.
Ya bayyana cewa gine-ginen da abin ya shafa masu hawa biyu ne dake da fadin kusan kafa 120 da kafa 125, wadanda ake amfani da su wajen sayar da robobi da wuraren ajiye kaya.
Daraktan ya ce gine-ginen da gobarar ta shafa sun hada da shaguna biyu a kasa, biyu a hawa na daya, shagunan ajiya shida da kuma shagunan wucin gadi hudu a saman bene.
Ya ce wutar ta tashi ne daga saman benen kafin ta bazu zuwa hawa na daya da kuma kasan gine-ginen da abin ya shafa.
Anas ya ce jami’an kashe gobara daga babban ofishin hukumar, da na Rijiyar Zaki, Sabon Gari, Gidan Gwamnati da rukunin Bompai sun yi nasarar kashe gobarar.
Ya kara da cewa wannan hadin gwiwa ta hana gobarar bazuwa zuwa sauran sassan fitacciyar Kasuwar ta Kofar Wambai.
Daraktan ya danganta faruwar lamarin da matsalar na’urar hasken rana ta sola, inda ya bayyana cewa gobarar ta yi barna ga shaguna da wuraren ajiye kaya da ke cikin gine-ginen da abin ya shafa.
Anas ya yi kira ga al’umma da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da daukar matakan kariya domin kauce wa faruwar gobara, musamman a kasuwanni da sauran wuraren da mutane suka yi yawa.
Haka kuma ya bukaci mazauna garin da ‘yan kasuwa da su samar da na’urorin gano gobara da na’urorin kashe gobara don aiki a gidajensu da shagunansu domin ba da damar gano wuta da shawo kanta cikin sauri. (NAN)













































