Kwamishinan Matasa, Wasanni da Rage Talauci na Jihar Borno, Saina Buba, ya janye kalaman da ya yi na barazana ga ‘yan adawa, sannan ya nemi afuwar jama’a.
SolaceBase ta ruwaito a baya cewa Buba, a cikin wani bidiyo da ya yadu, ya ce “Gwamnatin gwamnatinmu ce,” sannan ya kara da cewa duk wanda ya bi ta zai ji dadin zuma.
“Yanzu muna siyasa ne. Duk wanda ya nuna mana yatsa, mu ma za mu nuna masa. Duk wanda ya sake nuna mana yatsa, za mu karya masa yatsan,” in ji Buba.
Ya kara da cewa “Gwamnati gwamnatinmu ce. Wadanda suka bi mu za su ji dadin zuma, amma idan kuka ki, to za mu dake ku.”
Sai dai Buba ya janye kalaman kuma ya nemi afuwa a wajen taron manema labarai da ya kira, bayan sukar da ta biyo bayan bidiyon da ya yadu a ranar Laraba a Maiduguri.
A baya Kwamishinan ya fitar da bayanin, inda ya yi karin bayani game da bidiyon da ya shafi Shirin Tallafi na Kungiyar City Boy, wanda ya haifar da damuwa kan barazanar da kuma tsaron ‘yan adawa a jihar.
“A ‘yan kwanakin nan, wata magana da na yi a yayin shirin tallafi na Kungiyar City Boy a Maiduguri ta janyo cece-kuce tsakanin jama’a.”
“Ina so in bayyana a fili cewa ba nufina ba ne in cutar ko takura wa ‘yan jihar mu kan ‘yancin zabar jam’iyyar da suke so, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.”
“Ina mai jaddadawa cewa maganata ba ta wakiltar ka’idojin jam’iyyar APC ko gwamnatin Mai Girma Gwamna, Farfesa Babagana Umara Zulum ba.”
“Wannan gwamnati ba ta wulakanta hakkin ‘yan kasa, jam’iyya da gwamnati suna ci gaba da mutunta kowa, musamman matasa wadanda suka kasance masu goyon bayan jam’iyya da gwamnatin Zulum.”
“Gwamna Zulum da APC sun nuna jajircewa kan dimokuradiyya a tsawon shekaru bakwai da suka gabata, kuma hakan zai ci gaba har karshen mulkinsa.”
“A baya na bayyana cewa ba nufina a dauki maganata a zahiri ba. Amma ganin yadda cece-kucen ke ci gaba, ina amfani da wannan dama in janye kalamaina, sannan in nemi afuwa ga dukkan al’ummar Jihar Borno da ma ‘yan Najeriya baki daya kan duk wani bacin rai da kalamaina suka jawo.” in ji Kwamishinan.
(NAN)












































