Jami’ar Northwest ta gargadi jama’a game da sanarwar daukar dalibai 2026/2027 ta bogi, ta yi kashedi kan ‘yan damfara

Northwest University Sokoto new

Jami’ar Northwest ta Sakkwato (NWUS), ta gargadi masu neman gurbi, iyaye da masu kula da dalibai game da wata sanarwar daukar dalibai ta bogi da ke yawo a shafukan sada zumunta na intanet.

Gargadin na kunshe cikin wata sanarwa da Malam Abdallah El-Kurebe, Darakta mai kula da Sadarwa, Al’amuran Jama’a da Kariya na NWUS, ya fitar ranar Alhamis a Sakkwato.

Sanarwar ta ce takardar bogin ta na da’awar cewa jami’ar ta fitar da jerin sunayen daliban da aka dauka a zagayen farko da na biyu na shekarar 2026/2027.

Ta ce sanarwar ta bayar da lambar waya, 07073682223, kuma ta ambaci sunan wata “Dr. Mrs. Mary”, wadda ke umartar masu neman gurbi da su duba matsayin shigarsu makaranta, su yi rajista, su biya kudin makaranta, kuma su sami gurbi a zagaye na gaba.

Jami’ar ta bayyana sanarwar a matsayin ta damfara, kuma ta jaddada cewa ba ta fito daga makarantar ba.

“Ba ma bukatar masu neman gurbi da su biya kudi ga daidaikun mutane ta boyayyar hanya don samun gurbi ba, kuma ba mu bai wa mutane izinin amfani da lambobin wayoyinsu na don ba da gurbi, yin rajista, karbar kudin makaranta ko tabbatar wa masu nema gurbi a shirye-shiryen karatunmu ba,” in ji ta.

NWUS ta nuna damuwa kan yadda wasu marasa kishi ke kokarin amfani da damar burin masu neman gurbi da iyalansu na son shiga makaranta don su zalunce su.

Ta bukaci masu neman gurbi da mambobin jama’a da su yi watsi da lambar wayar da kuma umarnin da ke cikin sanarwar bogin, sannan su guji tura kudi ko bayyana bayanan sirrinsu na neman shiga makaranta ta hanyoyin da ba a amince da su ba.

Haka kuma, jami’ar ta shawarci masu neman gurbi da su yi hattara da mutanen da ke da’awar za su iya duba musu sunayen wadanda aka dauka, samo musu gurbi, taya su rajista, ko tabbatar musu da gurbi a madadinsu muddin za su biya kudi.

Ta ce duk wani bayani da ya shafi shigar dalibai, gami da fitar da jerin sunayen wadanda aka dauka, hanyoyin rajista, kudin makaranta da sauran sabuntawa na hukuma, za a fitar da su ne ta halatattun hanyoyin sadarwa na jami’ar.

Hukumar ta bukaci iyaye da masu kula da dalibai da su gargadi ‘ya’yansu da wadanda suke kulawa game da wannan damfara, sannan su tabbatar da bayanan da suka shafi shigar makaranta kai-tsaye daga jami’ar kafin su biya kowane irin kudi ko daukar wani mataki.

Jami’ar ta shawarci mambobinta da su tuntube ta ta halatacciyar lambar wayarta ta hukuma, 0704-269-9999, don tantance bayanan da suka shafi shigar dalibai.

Ta sake jaddada aniyarta na tabbatar da gudanar da aikin tantance dalibai a bayyane kuma cikin gaskiya, tare da kare masu neman gurbi da iyalansu daga hannun ‘yan damfara.

Hukumar ta bukaci jama’a da su yi watsi da sanarwar da ke yawo, kuma su dogara kadai da bayanan da aka fitar ta hanyoyin sadarwa na hukuma na jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here