Yanzu-Yanzu: Alkalin Babbar Kotun Kebbi Bunza da aka yi garkuwa da shi ya shaki iskar ‘yanci

High Court new

Alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi da aka yi garkuwa da shi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza ya koma cikin iyalinsa bayan ya shafe kusan mako guda a hannun masu garkuwar da suka yi garkuwa da shi.

Wani daga cikin iyalan Alkalin ne ya tabbatar da sakin nasa a ranar Litinin, inda ya ce Alkali ya iso gida lafiya da sanyin Safiya.

Mutumin ya bayyana dawowar Alkalin a matsayin wani lokaci na godiya.

“Mun cika da farin ciki da godiya ga Allah bisa dawo da shi lafiya. Mako guda ya kasance na kunci, amma a yau iyalinmu suna murnar dawowarsa,” in ji majiyar.

“Muna mika godiya ta musamman ga bangaren shari’a na jihar Kebbi, jami’an tsaro da al’ummar Jihar Kebbi baki daya da suka ba da gudummawa ta hanyoyi daban-daban, suka yi addu’a, suka tura sakonnin jaje. Kulawa da goyon baya, kuma muna godiya bisa hadin kan da kuka nuna,” in ji shi.

A cewar dan uwan, addu’o’i, kwarin guiwa da hadin kan da mutane da dama suka nuna ne ya kara baiwa iyalan kwarin gwiwar samun shi cikin koshin lafiya a lokacin da lamarin ya faru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here