FAAN ta tabbatar da tashin gobara a Terminal 2 na filin jirgin saman Legas

Screenshot 2026 08 02 085123 1785657100 609x430

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) ta tabbatar da faruwar gobara a Terminal 2 na Filin Jirgin Saman Murtala Muhammed na Kasa da Kasa da ke Legas.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a ranar Lahadi a shafinta na X, ta ce Ma’aikatan Ceto da Kashe Gobara na Filin Jirgin yanzu haka na amsa kiran gaggawa kuma na kokarin shawo kan lamarin.

Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa babu wani rauni ko asar rai da aka samu.

“FAAN tana son sanar da jama’a cewa an samu tashin gobara a Terminal 2 na Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed dake Legas.
Ba a samu rahoton rauni ko asar rai ba,” in ji sanarwar.

Hukumar ta kara da cewa za ta ci gaba da ba da sabbin bayanai da zarar an samu karin bayani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here