Zaben Fidda Gwani: NDC ta kafa kwamitin sulhunta ‘yan takara

NDC NDC

Jam’iyyar NDC ta sanar da wasu muhimman matakai da nufin karfafa demokiradiyya ta cikin gida, tabbatar da samun daidaito da kuma kafa jam’iyya mai karfi a matsayin dandalin siyasa gabanin zaben da ke tafe.

An cimma wannan matsayar ne a taron da Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na jam’iyyar yayi a karo na biyu, Sakataren Yada Labarai na Kasa Osa Director ya fitar da sanarwa a ranar Asabar.

A cewar bayanin jam’iyyar, duk gwamnatocin da aka zaba a karkashin tutar NDC za a bukaci su tuntubi tsarin jam’iyyar kafin su yanke manyan shawarar manufofi, nadin mukamai, da aiwatar da shirye-shirye, sai dai a kan nadin ma’aikatan sirri.

Jam’iyyar ta jaddada cewa ita ce gaba sama da bukatun mutum daya, tare da rokon mambobin jam’iyyar da su daidaita burinsu da ayyukansu da manufofi da akidar NDC.

A wani bangare na kokarin karfafa ladabtarwa a jam’iyyar, kwamitin zartarwa jam’iyya ya amince da kafa cikakkun ka’idoji da dokokin ga jami’an jam’iyya da ‘yan takara. An ba kwamitin da ke karkashin jagorancin Mai Baiwa Jam’iyyar Shawara kan Shari’a na Kasa umarni ya tsara tsari da jagororin aiwatar da ka’idar.

Jam’iyyar ta kuma sanar da kaddamar da Kwamitin Sulhu na Kasa wanda aikin sa zai kasance tattaunawa da sulhunta mambobin da abin ya shafa bayan al’amuran siyasa da zaben fidda gwani na kwanakin baya.

Kwamitin Zartarwa ya kara yanke hukunci cewa dukkan kungiyoyin da ke da alaka da jam’iyyar dole ne su yi aiki karkashin jagoranci da kula da jam’iyyar kuma kada su yi aiki daban ko daidai da tsarin jam’iyyar da aka kafa.

Ta sake jaddada kudurin ta na cimma nasara mai dorewa, ta kuma bayyana cewa ana gina ta ne a matsayin cibiya mai dorewa ba wata jam’iyya da ta dogara kan mutum daya, burin siyasa, ko ra’ayi na musamman ba.

Jam’iyyar ta roki mambobi su ci gaba da riko da akidarta da bayar da gudummawa wajen dorewarta ga tsararraki masu zuwa, tana mai jaddada cewa biyayya ga jam’iyya da bukatar kasa dole ne su fi son kai muhimmanci.

Kan kula da kudi, NDC ta yi alkawarin samar tsauraran hanyoyin bincike wurin amfani da kudaden jam’iyyar. Ta bayyana cewa dole ne a yi amfani da kudaden jam’iyyar don harkokin jam’iyya kawai, yayin da za a bukaci ‘yan takara a kowane mataki su bayyana cikakkun bayanai kan inda kudaden yakin neman zabe suka fito da masu bada gudummawa.

Bisa matsayar, dole ne a tura dukkan kudaden yakin neman zabe ta hanyar asusun yakin neman zabe na jam’iyya da aka ware a matakin kananan hukumomi, jihohi, yankuna, da na kasa, ciki har da asusun yakin neman zabe na shugaban kasa da na gwamna idan ya dace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here