Yan sanda sun gargadi masu hawa Takalmi Taya a kan hanyoyi da wuraren da aka haramta a Kano

img 4913 750x430

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta yi gargadi kan yawaitar matasa masu wasa da takalmin taya a kan manyan hanyoyin da wuraren da ake aikin hanyoyi da gadoji da sauran wuraren da aka haramta a cikin birnin Kano.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda, CSP Abdullahi Haruna-Kiyawa ne ya sanar da gargadin a cikin wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai a ranar Juma’a a Kano.

Ya ce duk da wasan takalmin wasa ne na nishadi, amma idan aka yi shi a kan hanyoyin da motoci ke wucewa cikin sauri, barazana ne mai ga rayuwar masu yin da sauran masu amfani da hanya.

“Rundunar ta lura da rashin jin dadi cewa matasa da yawa na shiga ayyuka masu hadari kamar rike motocin da ke tafiya domin yin sauri da nishadi.

Ya kuma cewa an tsara manyan hanyoyi ne don zirga-zirgar motoci kuma yin amfani da takalmin taya a kansu yana kawo tsaiko ga mota, lamarin da zai iya haifar da hatsarori.

Kakakin ya ƙara bayyana cewa amfani da takalmin a kan hanya na sanya duka masu hawa takalmin da direbobi cikin hadari.

’Yan sanda ba za su yi jinkirin kama wa da gurfanar da duk wanda aka samu yana hana zirga-zirga, jefa tsaron jama’a cikin hadari, ko shiga ayyukan da za su iya haifar da mummunan rauni ga kansu ko wasu ba. In ji shi.

Ya bukaci jama’a su bayar da rahoton duk wani wasan takalmin taya na rashin kunya ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta hanyar layukan gaggawa na Rundunar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here