Mustapha Sule Lamido, jigo a Jam’iyyar PDP, ya shiga takar gwamnan Jigawa a zaben shekarar 2027.
Lamido, dan fitaccen jigo a PDP kuma tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, ne ya bayyana hakan yayin da yake mika fom dinsa na takara ga jam’iyyar a ranar Talata a Dutse babban birnin jihar.
Shi ne kuma dan takar gwamnan PDP a zaben 2023.
A wancen zaben, dan takar APC kuma Gwamna mai ci a yanzu, Umar Namadi, ya samu kuri’u 618,449 wanda ya bashi damar yin nasara, sai Lamido na PDP ya zo na biyu da kuri’u 368,726, yayin da Ibrahim Ringim na NNPP ya samu kuri’u 37,156, lamarin da ya nuna zabe na tsakanin jam’iyyu uku wanda ya sauya yanayin siyasar Jigawa.
Lamido ya ce ya fito takar gwamna ne bayan tuntubar juna da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar.
Ya ce yana da imani da tsarin jam’iyyar, karfinta da juriyarta wajen magance matsalolinta na cikin gida da kuma magance matsalolin da ke addabar Najeriya.
“Muna da amincewa da jam’iyyarmu, kuma muna da yakinin cewa al’ummar Jigawa da Najeriya ma suna da amincewa da ita. Babu wata jam’iyya da ta taba kawo ayyuka da shirye-shiryen da suka inganta rayuwar ‘yan Najeriya kamar PDP,” in ji shi.
Ya zargi gwamnatin APC da gaza kawo tsare-tsaren da za su kawo ci gaba mai dorewa na zamantakewa da tattalin arziki a kasar.
Yayin da yake kira ga mambobin jam’iyyar da su mara masa baya, Lamido ya yi alkawarin ci gaba da tabbatar da manifofin jam’iyyar wadda ke dogaro kan kishin kasa da hidima ga dan adam. (NAN)










































