Jam’iyyaar APC ta sauya jadawalin zaben 2027, ta fitar da asusun biyan kudi

APC Flag

Jam’iyyar APC ta fitar da sabon jadawalin ayyuka da aka gyara na zaben shekarar 2027, ta sauya lokutan tantancewa, zabukan fidda gwani, korafe-korafe, da sauran matakan cikin gida na jam’iyya, yayin da ta kuma wallafa asusun banki da aka kebe don siyan fom din nuna sha’awa da tsayawa takara.

Sanarwar, wadda aka fitar ranar Litinin daga sakateriyar jam’iyya ta kasa, dake Buhari House, Abuja, wadda sakataren tsare-tsaren jam’iiayr na kasa, Sulaiman Muhammad Argungu, ya sanya wa hannu, kuma sakataren yaɗa labarai na, Felix Morka, ya tabbatar da ita tare da rarraba wa ga manema labarai.

Jam’iyyar ta bayyana cewa, “Bisa ga kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, dokar zabe ta shekarar 2026, da jadawalin ayyuka da aka gyara na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) na zaben shekarar 2027, jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin ayyuka da aka gyara na zabukan.”

A cewar jadawalin, za a fara sayar da fam daga ranar 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu na shekarar 2026, yayin da cike wa da dawo fa fam din ranar 4 ga Mayu na shekarar.

Za a fara tantance ‘yan takara daga ranar 6 ga Mayu zuwa 9 ga, wanda ya shafi ‘yan takarar majalisar dokokin jiha, majalisar wakilai, majalisar dattawa, gwamna da na shugaban kasa a matakai.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa, “korafe-korafen tantancewa na ‘yan majalisar dokokin Jiha da majalisar wakilai zai gudana daga ranar Talata 12 zuwa Laraba 13 ga Mayu.”

Zaben fidda gwani zai fara a ranar 15 ga Mayu, farawa da na majalisar wakilai, sannan na majalisar dattawa, majalisun dokokin Jiha, na gwamna da na shugaban kasa, wanda zai kare a ranar 23 ga Mayu, 2026.

APC ta kuma fitar da kudin fom din nuna sha’awa da tsayawa takara, inda ta bayyana, majalisar dokoki Naira 1,000,000 nuna sha’awa, sai kuma na tsayawa takara Naira 5,000,000. Yayin da majalisar wakilai Naira 1,000,000 sai kuma Naira 9,000,000 na tsayawa Takara

Sanarwar ta kuma ce majalisar dattawa Naira 3,000,000 na nuna sha’awa sai Naira17,000,000.

Inda kuma tace gwamna zai biya Naira 10,000,000 na nuna sha’awa sai kuma Naira 40,000,000 na tsayawa takara, yayin da shugaban kasa zai biya Naira 30,000,000 na nuna sha’awa da Naira 70,000,000 na Takara.

“Mata ‘yan takara, matasa da nakasassu za su biya kudin nuna sha’awa da kashi 50 cikin 100 na kudin tsayawa takara da aka kayyade na kowane matsayi.” Inji sanarwar.

APC ta umarci a biya dukkan kudade a cikin asusun jam’iyya da aka kebe, tana mai cewa, “Ya kamata a biya dukkan kudade gaba daya kai tsaye zuwa cikin asusun banki da aka kebe na Jam’iyyar ta APC kamar haka: Union Bank Plc -0239691733, UBA Plc – 1025098328, da kuma Zenith Bank Plc – 1014008105.”

Jadawalin da aka gyara ya zo ne yayin da jam’iyyun siyasa ke kara shiri don tunkarar zaben shekarar 2027 bisa tanadin da tsarin mulki, da dokar zaɓe ta shekarar 2026, da ka’idojin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta fitar, inda APC ke cewa gyare-gyaren na nufin tabbatar da tafiyar matakai na cikin gida cikin sauki da daidaita zaben fidda gwani na ta a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here