Wata babbar kotun jihar Kano ta soke takardar shaidar nasara da aka bai wa Alhaji Abdullahi Ghali-Shitu Basaf a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso.
Mai ƙarar, Ali Musa Danmalki, ta hannun lauyoyinsa Mista S.B. Wadau da Jazuli Mustafa, ya shigar da ƙara a kan waɗanda ake ƙara, yana ƙalubalantar matakin jam’iyyar NNPP na maye gurbinsa bayan ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Musa Danmalki ya roƙi kotu ta tabbatar da shi a matsayin sahihin ɗan takarar NNPP tare da bayyana maye gurbinsa a matsayin take dokokin zaɓe.
Haka kuma ya nemi kotu ta tabbatar da tsayawarsa takara a zaɓen ƙaramar hukumar Kumbotso.
Ya kuma zargi cewa duk da akwai umarnin kotu a baya, Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta ƙi bin umarnin, inda ta ci gaba da rantsar da Ghali-Shitu Basaf a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Abdu Maiwada-Abubakar ya soke takardar shaidar nasarar da aka bai wa Ghali-Shitu Basaf, yana mai cewa an yi hakan ne bisa saba wa umarnin kotu.
Kotun ta kuma soke dukkan matakan da waɗanda ake ƙara suka ɗauka waɗanda suka saɓa wa umarninta.
Haka zalika, Mai shari’a Maiwada-Abubakar ya umarci Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano da ta bi hukuncin kotu da aka yanke a ranar 25 ga Oktoba, 2024, tare da jaddada cewa dole ne a mutunta umarnin kotu.
Waɗanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da NNPP, Abdullahi Ghali-Shitu Basaf da kuma Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Musa Danmalki ya taɓa zuwa gaban babbar kotun Kano mai lamba 4, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Usman Na’abba, inda ya nemi a bayyana haƙƙinsa bayan da aka maye gurbinsa ba bisa ƙa’ida ba a matsayin ɗan takarar NNPP.
Ya bayyana cewa duk da an tsayar da shi, an tantance shi kuma ya sayi fom domin tsayawa takara a kujerar shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, amma daga baya aka maye gurbin sunansa da na Ghali-Shitu.
A wani hukunci da aka yanke a ranar 25 ga Oktoba, 2024, Mai shari’a Na’abba ya tabbatar da Musa Danmalki a matsayin sahihin ɗan takarar NNPP na kujerar shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso.











































