Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a sakatariyar tarayya da ke Abuja

Fire federal secretariat Abuja

Wani bangare na ginin Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ya kama da wuta.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an fara ganin wutar ne a wani bangare na ginin da misalin karfe 8:20 na safe, inda aka ga hayaki yana tashi daga wurin da abin ya shafa.

An ce lamarin ya faru ne a bangare na C na ginin ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, a cikin harabar ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, inda aka ga ma’aikatan da ke cikin ginin suna barin wurin da abin ya shafa yayin da aka sanar da jami’an agajin gaggawa domin shawo kan lamarin.

Sashen yada labarai na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa gobarar ta takaitu ne a bangare na C na ginin, kuma a halin yanzu jami’an agajin gaggawa na kokarin shawo kanta.

Har yanzu ba a gano ainihin musabbabin tashin gobarar ba, domin ana sa ran fara bincike kan abin da ya haddasa gobarar bayan an samu cikakken iko a kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here