Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa, an kawar da ‘yan bindiga da dama a lokacin da wasu jiragen saman soji na rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) suka harba makami mai linzami a wajen wani bikin aure da aka shirya wa daya daga cikin manyan ‘yan bindiga a Katsina.
A cikin wadanda aka kashe har da Sule, wani fitaccen shugaban ‘yan fashi, wanda kani ne ga Lalbi Ginshima wani babban dan fashi mai kisa.
Hare-haren da dakarun sojojin saman Najeriyar suka kai a kauyen Unguwar Adam da ke karamar hukumar Dan Musa a jihar.
Majiyar leken asiri a Katsina ta shaida wa PRNigeria cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne sojojin sama suka samu bayanan sirri cewa ‘yan ta’addan sun yi hijira daga Dan Alikima zuwa Unguwar Adam domin daurin auren daya daga cikin manyan shugabanninsu.
“Saboda haka, aka aike da jirgin sama nan a leken asiri don sa ido kan abubuwan da ke faruwa a wurin.
“Daga baya jirgin ya tabbatar da cewa gaskiya ne bayan an hango sama da mutane hamsin (50) na ‘yan fashin da ke yin bukukuwan.
“Saboda haka, an ba da rahoton halin da ake ciki kuma aka tura wani jirgin saman NAF don gudanar da aikin bindige mutane,” in ji wani babban jami’in leken asirin soja.
A cewar ma’aikacin jirgin na ISR ya ci gaba da bindige ‘yan ta’addan har zuwa wani wuri da ‘yan ta’addan suka gudu a Arewacin Unguwar Adam.
Ya ce: “Lokacin isowar jirgin, ya lura da ‘yan ta’adda sama da hamsin (50) tare da kama su da rokoki da bindigogi a jere.”
Wata majiya a cikin gida ta shaida wa PRNigeria cewa an yi wa yan bindigar mumunan barna inda aka kashe da yawa daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.
“’Yan ta’addan sun samu munanan raunuka inda 27 suka rasa rayukansu, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban. Daga cikin wadanda aka kashe har da shugaban ‘yan fashin Sule wanda kane ga babban dan fashin nan Lalbi Ginshima,” inji majiyar.












































