Gwamnatin tarayya ta musanta zargin kafa matatar zinari a Legas

Dele Alake

Gwamnatin tarayya ta musanta ikirarin da Ƙungiyar Tsofaffin Arewa ta yi na cewa an kafa matatar zinari a Legas ba tare da bin ka’idar daidaito tsakanin sassan ƙasa ba.

Ma’aikatar tarayya ta albarkatun ma’adinai ta bayyana cewa zargin da kakakin Ƙungiyar Tsofaffin Arewa, Farfesa Abubakar Jiddere ya yi , cikin wata sanarwar da ya sanya wa hannu wadda ba gaskiya ba ce.

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan albarkatun ma’adinai, Segun Tomori, ya fitar a Abuja, ta bayyana cewa ministan albarkatun ma’adinai, Dakta Dele Alake, bai taɓa sanar da cewa gwamnatin tarayya ta mallaki ko ta kafa wata matatar zinari a Legas ko a wani wuri ba.

Sanarwar ta jaddada cewa abin da ministan ya faɗa shi ne batun shirin ƙaddamar da wata matatar zinari, tare da bayyana cewa akwai wasu matatun zinari da ake shirin kafawa a sassa daban-daban na ƙasar, kuma dukkan su mallakar kamfanoni masu zaman kansu ne.

Tomori ya bayyana cewa sabuwar matatar zinari aikin kamfanin hakar ma’adinai mai zaman kansa ne gaba ɗaya mai suna Kian Smith, wanda ke da burin bunƙasa masana’antar zinari a cikin gida ta hanyar sabbin dabaru da ingantattun

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here