Rundunar ’yan sandan Najeriya ta dakatar da aiwatar da dokar hana izinin amfani da baƙin gilashin mota a fadin kasa, biyo bayan wani umarnin rikon kwarya da kotu ta bayar wanda ya hana fara aiwatar da matakin.
Rundunar ta bayyana cewa tun da farko ta sanar da shirin fara aiwatar da dokar ne bisa dalilin kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaron cikin gida a kasa, amma daga baya aka isar mata da umarnin rikon kwarya daga kotu da ya hana ci gaba da aiwatar da dokar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya sanya wa hannu, rundunar ta bayyana cewa kotu ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar har sai an saurari karar gaba daya ko kuma an janye umarnin.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa ta shiga cikin shari’ar a hukumance, ta gabatar da ƙalubalen farko, tare da neman kotu ta janye umarnin rikon kwaryar da aka bayar, inda kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci na gaba domin ci gaba da shari’a.
Sanarwar ta jaddada cewa dakatar da aiwatar da dokar na gudana ne bisa cikakken bin umarnin kotu da kuma mutunta ikon shari’a, har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe kan lamarin.
Babban sufeton ’yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya sake tabbatar da kudirin rundunar na kiyaye doka da oda tare da ci gaba da aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da hanyoyin tsaro na halal da suka dogara da bayanan sirri domin kare lafiyar jama’a da tsaron kasa.











































