Wata matar aure mai shekaru 20 Fatima Abdullahi, ta gurfana a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kano bisa zarginta da sace kayan abinci da tsabar kudi naira har Naira 250,000 mallakin wanda ya dauke ta aiki.
Wadda ake tuhumar din da ta kasance mazauniyar Unguwar Uku a Kano, ana tuhumarta ne da laifin sata.
Lauyan masu shigar da kara, Zahradeen Abubakar, ya shaida wa kotun cewa Yusuf Hassan, wanda ya shigar da kara ne ya kai karar a ranar 6 ga watan Mayu a ofishin ‘yan sanda na Hotoro.
Zahradeen Abubakar ya ce, wadda ake tuhumar tana aiki ne a gidan mai karar a matsayin mai aikace-aikace.
Amma amsa laifin da ake tuhumarta da aikatawa, Inda daga bisani Alkalin kotun, Malam Umar Lawal, ya bayar da belinta a kan kudi naira 30,000 tare da wanda zai tsaya mata mutum daya wanda dole ne ya kasance dan uwanta na jini.
Mai shari’a Umar Lawal ya kuma dage ci gaba da sauraren karar har sai ranar 19 ga watan Yuni.
NAN













































