EFCC ta kama tsohon dan majalisa Gudaji Kazaure bisa karbar Naira miliyan 70 daga hannun Emefiele

Gudaji Kazaure 750x430

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama tsohon dan majalisar wakilai Gudaji Kazaure bisa zargin karbar naira miliyan 70 daga hannun tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.

Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kama Kazaure a ranar Larabar da ta gabata jim kadan bayan wata babbar kotun Kano ta ba da umarnin dakatar da tsohon dan majalisar.

A cewar wata majiya a hukumar ta EFCC, Kazaure ya karbi Naira miliyan 20 a kashi biyu ta hannun jakadan Emefiele mai sun Eric domin sayen Ragunan Sallah.

Majiyar ta ci gaba da cewa Kazaure daga baya ya karbi kudi Naira miliyan 50 a matsayin “gudunmawa” daga Emefiele, biyo bayan wata gobara da ta tashi a gidan tsohon dan majalisar.

Karin karatu: Da ɗumi-ɗumi: EFCC ta saki VeryDarkMan

Majiyar ta ce Kazaure a halin yanzu yana tsare a ofishin hukumar da ke Kano kuma ana iya kai shi Abuja domin fuskantar tuhuma.

A watan Disambar 2022, Kazaure ya zargi gwamnan CBN na lokacin da almundahana, inda ya yi zargin cewa an batar da Naira tiriliyan 89.1 na Tambarin aiki a karkashin Emefiele.

Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa da gangan aka hana shi gabatar da rahoton share fage na kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin nazarin kudaden harajin tambarin da CBN ke rike da shi.

Fadar shugaban kasa a wancan lokaci awata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu, ya fitar, ta musanta zargin da Kazaure ya yi cewa ba gaskiya ba ne, inda ya kara da cewa kwamitin da aka ce tun daga lokacin ne aka rusa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here