Najeriya ta samu dala biliyan 1.3

Najeriya, dala, biliyan, bashin, samu
Najeriya ta samu bashin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke jamhuriyar Nijar, kamar yadda ma'aikatar sufurin...

Najeriya ta samu bashin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi da ke jamhuriyar Nijar, kamar yadda ma’aikatar sufurin kasar ta sanar ranar Laraba.

Layin na dogon dai zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen guda biyu ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.

Karin labari: Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya bude iyakoki

Ma’aikatar sufurin ta Najeriya ta ce kamfanin gine-gine na kasar China, CCECC, shi ne zai samar da kaso 85 na yawan kudaden.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Najeriya da hadin gwiwar bankin Africa Export-Import Bank da bankin habaka tattalin arzikin Afirka na Africa Development Bank.

Karin labari: Hisbah ta kama wadanda ba sa yin azumi a jihar Kano

“Samun bashin na dala biliyan 1.3 na nuni da irin nasarar da za’a samu wajen kammala layin dogon” in ji sanarwar.

Wannan dai na daya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Najeriya na inganta harkar sufuri a fadin kasar domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here