Mahara sun kashe sama da 70 a Filato

Black Christmas In Plateau As Marauders Kill Over 70 In Fresh Attack
Black Christmas In Plateau As Marauders Kill Over 70 In Fresh Attack

Sama da mutane saba’in da shida ne rahotanni suka ce maharan sun kashe a wasu sabbin hare-hare da aka kai a wasu kauyukan kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato.

Shugaban kwamitin zartarwa na karamar hukumar Bokkos ne ya shaidawa gidan Talabijin na Channels cewa yan bindigar sun fara kai hare-haren hadaddiyar ne a ranar Asabar da ta gabata har zuwa jajibirin Kirsimeti a lokacin da mazauna yankin ke cikin shagalin biki.

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa adadin wadanda suka mutu yana karuwa yayin da tawagar jami’an tsaro,  da mafarauta suka bi daji domin neman wadanda suka bata sakamakon hare-haren.

Ya kara da cewa maharan sun kona gidaje da dama wadanda kuma suka yi awon gaba da amfanin gona tare da lalata dukiyoyi a cikin kauyikan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here