EFCC ta gurfanar da Fani-Kayode a gaban kotu

E6E30C58 2DB8 4A41 99AB 1BD3FB7FBEB1
E6E30C58 2DB8 4A41 99AB 1BD3FB7FBEB1

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta gurfanar da tsohon ministan jiragen sama Femi Fani-Kayode a gaban wata kotu dake Ikeja a jihar Legas bisa zargin gabatar da takardun lafiya na bogi.

EFCC ta gabatar da laifuka 12 da take zargin tsohon ministan da aikawata wanda suka hada da bayar takardun shaida na bogi.

Lauyan wanda ake kara Wale Balogun ya kalubalanci kotun da cewa bata da hurumi na sauraron wannan karar, inda ya bukaci kotun ta kori karar.

Ya kara da cewa laifukan da ake zargin Kayode da aikatawa an yi su ne a Abuja, don haka babu wata kotu a Legas dake da hurumi na sauraron karar.

Yayin da yake maida martani kan wannan zargi, Lauyan EFCC  Rotimi Oyedepo ya bukaci kotun tayi watsi da bukatar lauyan wanda ake kara, yana mai cewa sashe na 393 na kundin dokar gudanar da mulki ta shekarar 2015 ya bawa wannan kotun damar sauraron irin wannan karar.

Mai Sharia O.O Abike-Fadipe ta dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Disamba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here