Kamfanin WhatsApp Ya Sanar Da Wani Sabon Cigaba.

August 24, 2021, Brazil. In this photo illustration the WhatsApp logo seen displayed on a smartphone

Shugaban rukunin kamfanin Meta dasuka kunshi facebook da WhatsApp ya fidda sanarwar da fitar da wata sabuwar fasaha ga masu amfani da manhajar wajan gyara saƙonnin da suka aika.

WhatsApp ya fitar da wata sabuwar fasaha wadda za ta baiwa masu amfani da manhajar damar gyara sakonnin da suka aika.

Dangane da wannan sabuwar fasaha, masu amfani da manhajar za su iya gyara saƙonni ko da yakai minti 15 bayan an aika shi, Shugaban Kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, ya bayyana hakan a wannan Litinin.

“Duk lokacin da kuka yi kuskure ko kuma kawai ku ka canza ra’ayi, yanzu kuna iya gyara saƙonnin da kuka aika a WhatsApp.

“Muna farin ciki sanarda ku cewa yanzu kuna dama akan maganganunku da ku kayi, kamar gyara rubutun da ba daidai ba ko ƙara ƙarin bayani akan saƙo.

“Don haka, a cikin mintuna 15 da ku ka aikeda saƙon, dole ne ku matsa kuma ku riƙe wannan saƙon na ɗan lokaci sannan zaɓi zaɓi na ‘Edit’ daga menu.”

Kafin wannan sabuwar fasaha, masu amfani da WhatsApp kan goge saƙonni dungurungum kasancewar babu wata dama na iya yin gyara akan sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here