Jam’iyyar PDP ta dakatar da shugaban ta Iyorchia Ayu

Ayu 1 e1651259329668
Ayu 1 e1651259329668

Jam’iyyar PDP ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Iyorchia Ayu.

Shugaban mazabar Igyorov dake karamar hukumar Gboko ta jihar Benue ne ya dakatar da Dakta Ayu.

Da yake jawabi ga manema labarai, a madadin Kashi Philip, shugaban gundumar, sakataren gundumar Mr. Vangeryina Dooyum ya bayyana cewa kwamitin zartaswa ya dakatar da Dr. Ayu bisa zargin cin amanar jam’iyya.

Ana kuma zargin Ayu da rashin biyan hakokin ‘yan jamiyya na shekara kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada. Sha biyu daga cikin mambobin exco goma sha bakwai ne suka rattaba hannu kan takardun da ke tabbatar da dakatar da shi.

Sun kuma yi zargin cewa jigon PDP bai kada kuri’a ba a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

A cewarsu, yawancin makusantan Ayu sun yi aiki ne da jam’iyyar adawa ta APC wanda hakan ya haifar da mummunar faduwa ga PDP a mazabar Igyorov.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here