Ƴan sanda sun gurfanar da mutumin da ya shaƙe budurwarsa ta mutu ya kuma binne gawar

police 1 750x430 1
police 1 750x430 1

Ƴansanda a jihar Enugu sun kama wani mutum da ake zargi da shake budurwarsa tare da binne gawarta.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar, Daniel Ndukwe, a jiya Litinin a Enugu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Afrilu a unguwar Amori da ke karamar hukumar Nkanu ta Yamma a jihar.

Ya bayyana cewa an gurfanar da wanda ake zargin, mai shekaru 24, dan asalin Ebonyi, mazaunin Ogidi da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a Anambra, kuma an tsare shi a gidan yari na Enugu.

“Wanda ake zargin da marigayiyar sun tafi Amiru ne daga Ogidi, Anambra, a ranar 1 ga Afrilu zuwa wajen wani boka.

“A cikin dare, sun bar gidan noman zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“An ta neman su, amma ba a same su ba sai da safe, lokacin da ƴansanda su ka kama wanda ake zargin a unguwar Obe da ke yankin karamar hukumar, yayin da yake kokarin tserewa ya koma Ogidi,” in ji shi.

Ndukwe, mai muƙamin mataimakin sufeton yansanda, ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin shake mamaciyar tare da binne gawar a cikin jeji inda aka tono ta.

Ya kuma bayyana cewa an ajiye gawar a dakin ajiyar gawawaki domin a yi bincike a kanta.

“An mayar da batun zuwa sashin kisan kai na sashen binciken manyan laifuka na jihar Enugu, kuma wanda ake zargin ya gurfana gaban kotu,” Mista Ndukwe ya bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here