Ɗalibai 420,415 cikin su miliyan 1.95 ne kaɗai da suka rubuta UTME suka samu maki sama da 200 – JAMB

JAMB Exam

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan (JAMB) ta ce cikin dalibai miliyan 1,955,069 da suka rubuta jarrabawar a shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 ne suka samu kasa da 200 a jarrabawar.

Hukumar ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025, a shafin ta na X.

SolaceBase ta rawaito cewa kididdigar JAMB na sakamakon jarabawar UTME na shekarar 2025 da aka fitar a ranar Litinin ya nuna cewa ‘yan takara 420,415 ne kawai suka samu maki sama da 200 a cikin adadin na shekarar 2025 a UTME.

Yayin da dalibai 4756 suka samu sama da maki 320, sai kuma ɗalibai 7658 da suka samu maki tsakanin 300 da 319, daga jimillar ɗalibai 1,955,069 da suka rubuta jarrabawar a bana.

Bugu da kari, hukumar ta ce, akwai dalibai 71,701 da ba su samu damar halartar jarrabawar ba. Haka kuma wadanda ke fuskantar kalubalen gwajin yatsa “biometric” ana gudanar da bincike, kuma za a sanar musu lokacin da za su je cibiyoyin da aka kebe domin yin jarrabawar,” in ji Hukumar.

Hukumar ta bayyana cewa an kama dalibai 97 da laifin tafka magudin jarrabawa kai tsaye, yayin da a yanzu haka ana kan binciken wasu 2,157 da ake zargi da aikata ba daidai ba.

Hukumar JAMB ta jaddada cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da jarrabawar musamman ga makafi da kuma wadanda ke karkashin kungiyar JAMB Equal Opportunity Group (JEOG).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here