Yan majalisar wakilai sun musanta karbar Dala 5,000 don amincewa da ɗokar ta ɓaci a jihar Rivers

Reps Reps 750x430

Majalisar wakilai ta musanta zargin cewa an baiwa kowane dan majalisa dala 5,000 don amincewa da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu kan ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers.

Mataimakin kakakin majalisar, Hon. Philip Agbese daga jihar Benue na jam’iyyar APC yayin da yake mayar da martani kan batun a wata hira da manema labarai a Abuja ranar Asabar, ya bayyana zargin a matsayin karya da yunkurin bata suna.

A cewar Agbese, kudurin ranar Alhamis da majalisar ta yanke kan ayyana dokar ta-baci a Rivers anyi ne saboda kishin kasa da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Rivers.

Ya ce a matsayinsu na ‘yan majalisar masu sha’awar zaman lafiya da jin dadin al’ummar jihar Rivers, mun amince da dokar ta-baci ne saboda kishin kasa ba don wani kudi ba kamar yadda ake zargi.

Karin karatu: Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana matsayarsu kan dokar ta-baci a Rivers

Ya ce majalisar a cikin hikimar ta ta yi wasu muhimman gyare-gyare ga dokar ta-bacin da Shugaban ya yi kafin ta amince da shi.

Agbese ya ce ya yi imanin cewa Tinubu a matsayinsa na mai bin tafarkin dimokuradiyya na gaskiya ba zai yi yaki da dimokuradiyya a kasar nan ba.

Dan majalisar na Benue ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba su irin goyon bayan da suke ba su, tare da ba da tabbacin cewa za su yi aiki da muradun jama’a.

Ya kuma bayyana fatansa cewa a karshen dokar ta-baci, gwamnatin jihar Rivers da majalisar dokokin jihar za su dawo da karfi domin ci gaban jihar baki daya.

Dangane da cece-kucen da ake yi kan yawan kuri’u, Agbese ya ce majalisar ta cika sharuddan da ake bukata na yawan kuri’u da wakilai 243 da suka halarci taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here