Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun harbe wani matashi mai suna Khalid Bichi a Maitama, Abuja, a daren Juma’a.
Bichi, wanda aka ce ma’aikaci ne na Hukumar Tara Haraji ta Cikin Gida ta Tarayya, an bayar da rahoton cewa maharan sun kashe shi ne daf da karfe 9 na dare a lokacin da ya ke neman abinci, in ji Guardian.
Rahotanni sun ce an harbe shi sau da dama.
Daga nan ne aka garzaya da shi babban asibitin Maitama, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Za a yi jana’izar marigayin a yau da karfe 1:30 na rana bayan sallar jana’izar da aka yi a Abuja National.