Jirgi Ya Sake Kaucewa Daga Titin Jirgin Sama na Legas

Murtala Muhammed International Airport Lagos 1

A ranar Asabar din da ta gabata ne wani jirgin sama na kamfanin jiragen sama na Xejet ya tsallake titin jirgin a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas.

Jirgin XeJet E145 mai lambar rajista, 5NBZZ, da misalin karfe 11.29 na safe ya kauce daga titin jirgin zuwa bakin ciyayi a daidai lokacin da ya sauka.

Jirgin E145 ya taso ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja dauke da fasinjoji 52 da ma’aikatansa biyu.

“An sami nasarar kwashe fasinjojin. A halin yanzu an rufe Runway18L don zirga-zirga, “in ji wata majiya

Hukumar binciken tsaron Najeriya NSIB ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tura jami’anta zuwa wurin.

Wannan ci gaban ya zo ne makonni uku bayan da wani jirgin saman Dana ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman Legas.

Daga baya hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA ta dakatar da ayyukan kamfanin tare da bayar da umarnin gudanar da bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here