Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatocin jihohin kasar nan da su gina gidajan gyaran na zamani domin dakile cunkoso a gidajen gyaran hali da su, domin dakile matsalar fasa gidajen yari.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da cibiyoyi na garambawul, Chinedu Ogah, ya bayar da wannan shawarar a ranar Juma’a a lokacin da kwamitin ya ziyarci gidan yarin Suleja domin duba irin barnar da ruwan sama ya haddasa wanda ya yi sanadiyyar tserewa fursunonin daga gidan yarin.
Ogah ya kuma yi kira da a inganta ciyar da fursunonin da kuma daukar karin ma’aikatan aikin daza suyi aiki a gidajen.