Wasu rahotanni na nuna yiwuwar Sojin da ke mulki a jamhuriyyar Nijar su iya amincewa da sakin hambrarren shugaban kasar Bazoum Mohamed da iyalinsa kowanne lokaci daga yanzu.
Mabanbantan majiyoyi daga cikin Nijar da makwabciyarta Najeriya sun tabbatarwa jaridar Daily Trust shirin sakin hambararren shugaban cikin watan da muke ciki na Ramadana.
A cewar bayanan har yanzu akwai dambarwar dangane da bukatar hambararren shugaban ta ci gaba da zama a cikin Nijar ba tare da fitarsa kowacce kasa ba, wanda shi ne dalilin da ya kai ga gaza sakinsa har a wannan lokaci.
Karin labari: Giwa ta tattake wani jagoran yawon buɗe ido a Afirka ta Kudu
Bazoum dai na samun cikakken goyon bayan shugaba Emmanuel Macron na Faransa da kuma kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da jagoranta Bola Ahmed Tinubu dalilin da ake ganin shi ya sake tsaurara matakan sakin nasa daga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar ta yankin Sahel.
Tun bayan hambarar da gwamnatin ta Bazoum Mohamed a watan Yulin da ya gabata, Nijar ta gamu da zafafan takunkumai daga Faransa da ECOWAS lamarin da zafafa alaka tsakanin Nijar da makwabciyarta Najeriya karkashin jagorancin Tinubu.
Karin labari: Gwamnan Kano ya karbi bakuncin tawagar bankin Duniya
Baya ga Nijar ECOWAS ta kuma lafta wasu zafafan takunkuman kan Mali da Burkina Faso suma duk wadanda ke fuskantar mulkin Soji.
Wata majiyar diflomasiyya da kuma bangaren ‘yan jaridu sun tabbatarwa Daily Trust batun fara tattaunawar don sakin hambararren shugaban Bazoum Mohamed kowanne lokaci daga yanzu.
Karin labari: Burtaniya ta haramtawa ‘yan Najeriya da ma’aikatan lafiya zuwa kasashen waje
Jaridar ta kuma kafa hujja da wata fitacciyar jaridar Nijar da ake wallafawa a harshen Faransanci wadda ita ma ta yi dogon sharhi game da shirin sakin Bazoum amma bisa sharadin fitarsa don ci gaba da rayuwa a wata kasa, batun da hambararren shugaban ya ki amincewa.
Tun a cikin watan Yulin bara ne dai Sojojin na Nijar suka tsare hambararren shugaba Bazoum da maidakinsa da kuma dansa Salem gabannin sakin dan nasa a ranar 9 ga watan Janairun shekarar nan.