Shugaban Amurka ya yi barazanar ƙaddamar da hari a Najeriya sakamakon zargin kisan Kiristoci

Trump 1

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya umurci ma’aikatar yaƙin ƙasar su shirya don yiwuwar kai hari domin kawar da ‘yan ta’addan Musulmai a Najeriya.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social ranar Asabar, Trump ya gargadi gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kawo ƙarshen abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi da taimako da take bai wa Najeriya muddin gwamnati ta kasa dakile wannan matsala.

Trump ya ce idan gwamnatin Najeriya ta ci gaba da yin shiru kan lamarin, Amurka za ta iya kai hari cikin gaggawa domin hallaka ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci, yana mai cewa umarni ya riga ya bai wa ma’aikatar yaƙi domin shirya kai hare-hare cikin sauri da tsanani.

Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin yiwa Kiristoci kisan gilla da Amurka ta yiwa Najeriya

Wannan lamari ya zo ne kwana guda bayan da Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take hakkin addini, inda ya bayyana cewa Kiristoci na fuskantar kisan gilla daga masu tsattsauran ra’ayi.

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani da cewa Najeriya ƙasa ce ta dimokuraɗiyya da ke girmama ’yancin addini da imani, don haka ya ƙi amincewa da matakin da Trump ya ɗauka na sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ake zargi da wariyar addini.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here