SERAP ta maka Tinubu a kotu kan dakatar da Fubara, mataimakiyarsa, da ‘yan majalisa

SERAP Tinubu

Ƙungiyar kare hakkin al’umma da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta maka shugaban kasa Bola Tinubu a kotu kan dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokoki abinda ya kira an yi shi ba bisa ka’ida ba.

SERAP ta yi zargin cewa matakin ya saba wa tanadin tsarin mulki da kuma bata tsarin mulkin dimokradiyya.

Mambobin kungiyar SERAP’s Volunteers’ Lawyers Network (SVLN) a jihar Rivers ne suka shigar da karar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Juma’a.

Cikin wadanda ake kara hadar da babban Lauyan tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin wadanda ake tuhuma.

Karar mai lamba FHC/ABJ/CS/558/2025, ta bukaci “a ba da umurnin dakatar da hukuncin da shugaban kasa ya yanke a kan zababbun jami’an dimokradiyya a jihar Rivers a lokacin da ya ayyana dokar ta-baci da kuma “umarnin a yi watsi da nadin Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Shugaban da zai ja ragamar jihar Rivers.”

SERAP, a cikin wata sanarwa da mataimakin saraktanta Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi, ta bayar da hujjar cewa “dakatarwar ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma wajibcin shari’a na kasa da kasa, inda ta buga misali da Yarjejeniya ta Afirka kan ‘Yancin dan Adam da kuma Yarjejeniya Ta Afirka kan Dimokuradiyya, Zabe, da Mulki.

Karin karatu: Dakatar da gwamnan Rivers ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya – Jonathan

Ya kara da cewa sashe na 305, wanda ya baiwa shugaban kasa ikon ayyana dokar ta-baci, “bai cika ka’ida ba, ko kuma sama da sauran tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar,” yana mai jaddada cewa dole ne a yi amfani da irin wannan iko ta hanyar da za ta tabbatar da shigar dimokradiyya.

Daga cikin sauran agajin da ake nema, masu shigar da kara suna neman kotu don bayyana cewa matakin Tinubu “ba bisa ka’ida ba ne, kuma ba shi da amfani, da kuma neman a bada umarnin hana shugaban da aka nada shi kadai daga yin aiki a wannan matsayi.

“Sai dai a cikin sanarwar ba a sanya ranar da za a saurari karar ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here