Sarkin Musulmi ya yi umarnin a fara duban jinjirin watan Shawwal
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’ummar Musulmi a fadin kasar nan da su sanya ido kan ganin jinjirin watan Shawwal 1446AH a ranar Asabar 29 ga Maris, 2025.
Wannan na zuwa ne gabanin bukukuwan Sallah karama.
Sarkin Musulmi ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a 28 ga Maris, 2025.
SolaceBase ta ruwaito cewa ganin jinjirin wata zai tabbatar da kawo karshen watan Ramadan da kuma gudanar da ayyukan Eid al-Fitr.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ranar 29 ga watan Maris ita ce ranar 29 ga watan Ramadan shekara ta 1446, wanda ya zama ranar farko na fara duban jinjirin wata.
“Sarkin ya bukaci duk wanda ya ga watan da ya kai rahoto ta hanyar lambobin wayar da aka sanya a cikin sanarwar kamar haka: 08037157100, 08066303077, 08035965322, 08035945903 da 07067146900.
Sanarwar ta ce Majalisar Sarkin Musulmi za ta sanar da matakin karshe na ranar Eid-el-Fitr bisa tabbatar da ganin wata.